Sudan Ta Kudu Ta Amunce Da Tayin Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya amince da shirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya akan tura Karin sojojin kiyaye zaman lafiya dake da nauyin tabbatar da tsaro a wannan jinjira kasa da rikici ya daidaita.
Wanann dai na zuwa ne bayan rarrashin gwamnatinsa da kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na ganin ya amince da shirin tura Karin dakarun samar da zaman lafiya dubu hudu dan magance tashe tashen hankulan da ake samu a Juba babban birnin kasar da kewayensa.
A ranar Juma'a data gabata ce wata tawagar wakilan MDD ta ziyarci Juba babban birnin kasar domin jaddada muhimmancin kai dakarun dan kare lafiyar fararen hula da kuma dubban mutanen da rikicin ya raba da gidajen su.
A cen baya dai Gwamnatin Sudan ta Kudu a sahun gaba shugaban kasar Salva Kiir da sabon mataimakinsa Taban Deng sun ki amincewa da shirin aikewa da karin dakarun wanzar da zaman lafiyar 4,000 inda su ke bayyana hakan a matsayin wani yanayi na yunkurin mamaye kasar.
MDD ta dai dau kudirin aikewa da karin dakarun ne galibi na kasashen Afrika domin tabbatar da tsaro a Juba babban birnin kasar inda rikici ya barke tsakanin dakarun dake biyaya ga shugaba Salva Kirr da kuma tsohon mataimakinsa kana jagoran 'yan tawayen kasar Riek Machar a cikin watan Yulu daya gabata lamarin da yayi sanadin mutuwar daririwan mutane tare da cilasatawa dayewa tserewa daga gidajensu.