MDD Ta Bukaci A Kawo Karshen Rikicin Bayan Zabe A Kasar Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10612-mdd_ta_bukaci_a_kawo_karshen_rikicin_bayan_zabe_a_kasar_gabon
Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwa game da tashin hankalin da ya barke bayan zaben shugaban kasar Gabon, kana ya yi kira da'a gaggauta kawo karshen tashin hankalin a fadin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 05, 2016 01:24 UTC
  • MDD Ta Bukaci A Kawo Karshen Rikicin Bayan Zabe A Kasar Gabon

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwa game da tashin hankalin da ya barke bayan zaben shugaban kasar Gabon, kana ya yi kira da'a gaggauta kawo karshen tashin hankalin a fadin kasar.

Ban, wanda a yanzu haka yake birnin Hangzhou a gabashin kasar Sin, a taron koli na kungiyar kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya G20, inda ya zanta da shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ta wayar hannu, da kuma Jean Ping, dan takarar shugabancin kasar na Jam'iyyar DNP, ya bukace su da su kawo karshen tashin hankalin kasar.

Babban sakataren ya nuna muhimmancin amfani da hanyoyi na shari'a wajen warware duk wani rikici da ya shafi sakamakon zaben shugaban kasar.

Mai magana da yawun mista Ban ya ce, tuni ya umarci wakilin MDD na musamman dake Afrika ta Tsakiya, Abdoulaye Bathily da ya cigaba da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa domin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.