Kotu A Mauritaniya Ta Yanke Hukuncin Dauri Kan 'Ya'yan Tsohon Shugaban Kasar
Wata kotu a kasar Mauritaniya ta yanke hukunci dauri a gidan kurkuku kan 'ya'yan tsohon shugaban kasar bayan ta same su da laifin fataucin muggan kwayoyi.
Majiyar shari'ar kasar Mauritaniya ta sanar da cewa: Kotun da ke birnin Nouakchott fadar mulkin kasar ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku na tsawon shekaru 15 da kuma 6 kan Sidi Muhamed Wuld Haidalla da Sheikh Wuld Haidalla 'yayan tsohon shugaban kasar ta Mauritaniya Mohammed Khouna Wuld Haidalla bayan ta same su da hannu dumu -dumu a harkar fataucin muggan kwayoyi.
Muhammed Khouna Wuld Haidalla ya rike shugabancin Mauritaniya daga shekara ta 1980 zuwa 1984 miladiyya.
Sauran mutanen da suke da hannu a hada -hadar muggan kwayoyin an daure wasu shekaru 11 zuwa 9 musamman saboda rashin cikakkun shaidu kan sauran zarge-zargen da ake yi kansu.