Ministan Shari'ar Kasar Gabon Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10669-ministan_shari'ar_kasar_gabon_ya_yi_murabus_daga_kan_mukaminisa
Ministan shira'ar Gabon ya yi murabus daga kan mukaminsa domin nuna rashin amincewarsa da abin da ya kira rashin mutunta tsarin dimokaradiyya a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 06, 2016 01:13 UTC
  • Ministan Shari'ar Kasar Gabon Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminisa

Ministan shira'ar Gabon ya yi murabus daga kan mukaminsa domin nuna rashin amincewarsa da abin da ya kira rashin mutunta tsarin dimokaradiyya a kasar.

A ganawarsa da gidan radiyon Faransa a jiya Litinin Ministan shari'ar Gabon Seraphim Moundounga ya bayyana cewa ya yi murabus daga mukaminsa ne sakamakon matakin da gwamnatin Gabon ta dauka na rashin nuna damuwa ga matakan zaman lafiya da mutunta tsarin dimokaradiyya tun bayan bullar tarzoma a kasar sakamakon shelanta shugaba Ali Bango a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shugabancin kasar.

Rikici da tarzoma sun kunno kai ne a kasar Gabon tun bayan da ministan harkokin cikin gidan kasar ya shelanta shugaba Ali Bango Ondimba a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shugaban kasa da a gudanar a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata lamarin da ya tunzura 'yan adawa karkashin jagorancin Jean Ping tsohon shugaban gudanarwa ta kungiyar tarayyar Afrika da ya yi da'awar lashe zaben, inda suka fito zanga-zanga kan zargin tafka magudi a zabukan lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku a cewar gwamnatin kasar, yayin da majiyar 'yan adawa ke cewa mutanen da suka mutu sun kai goma tare da jikkata wasu daruruwa na daban baya ga kame wasu kimanin mutane 1000.