Shugaban Angola Ya Tsige Ministan Kudin Kasar Daga Kan Mukaminsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10672-shugaban_angola_ya_tsige_ministan_kudin_kasar_daga_kan_mukaminsa
Fadar shugaban kasar Angola ta sanar da cewa: Shugaba Jose Eduardo dos Santos ya tsige ministan kudin kasar daga kan mukaminsa biyo bayan matsalar tattalin arziki da Angola ta shiga sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 06, 2016 01:14 UTC
  • Shugaban Angola Ya Tsige Ministan Kudin Kasar Daga Kan Mukaminsa

Fadar shugaban kasar Angola ta sanar da cewa: Shugaba Jose Eduardo dos Santos ya tsige ministan kudin kasar daga kan mukaminsa biyo bayan matsalar tattalin arziki da Angola ta shiga sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya.

Babu wani kwakkwaran dalili da fadar shugaban kasar ta gabatar kan tsige ministan kudin kasar Armando Manuel dan shekaru 44 a duniya daga kan mukamin nasa bayan tsawon shekaru uku da yayi yana rike da mukamin minista.

A bayan sanar da tsige Armando Manuel an maye gurbinsa da Augusto Archer dan shekaru 53 a duniya kuma tsohon shugaban Hukumar kula da sanya hannun jari a kasar.

Tun bayan faduwar farashin dayen man fetur a kasuwannin duniya kasar Angola kamar saurar kasashen da suka dogara da mai a harkar tattalin arzikin kasarsu ta shiga cikin masifar tattalin arziki tare da faduwar darajar kudin kasar warwas a gaban dalar Amurka lamarin da ya kara wurga al'ummar Angola cikin tsananin rayuwa, kuma tun a cikin watan Yunin wannan shekara gwamnatin kasar ke zawarcin Bankin Bada Lamuni na Duniya na {IMF} kan neman bashin kudade da nufin rage radadin matsalar tattalin arzikin kasar.