Kungiyar Tarayar Afirka ta bayyana shirinta na taimakawa kasar Gabon
Kungiyar Tarayar Afirka ta bayana shirin ta na shiga tsakani wajen magance rikicin da ya kuno kai bayan zabe a kasar Gabon
A wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar tarayar Afirka AU ta ce , Shugaban Kasar Tchadi kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Idriss Deby Itno na bin dindingin abinda ke faruwa a kasar Gabon bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 31 ga watan Agusta a tsinake, sannan kungiyar AU din tare da hadin gwiwar kasashen yankin a shirye su ke su shiga tsakani, tsakanin bangarorin dake jayayya da juna da nufin samar da mafita dangane da rikicin.
Shugaban AU din ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar za ta shirya wata tawaga ta musaman wacce za ta hada shugabanin kasashe da shuganin kwamitin kungiyar zuwa kasar Gabon domin tattaunawa tare da shugaban kasar da kuma bangaren 'yan adawa da nufin samar da mafita na rikcin da kasar ke fama da shi.
Tun bayan sanar da sakamakon zaben kasar Gabon ne 'yan adawa suka bayyana rashin amincewar su da shi, inda suka gudanar da gagarumar zanga-zanga har ma suka cinnawa Majalisar Dokokin kasar wuta,ko baya ga hakan, rikicin ya lashe rayukan fararen hula tare da jikkata wani adadi mai yawa, sannan kuma Gwamnati ta kame sama da mahalta zanga-zangar dubu daya.