An bayana damuwa kan wanzuwar annobar kwalara a D/Congo
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana damuwar ta kan wanzuwar annobar kwalara a kasar D/Congo
Kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (OMS) ta bayyana cewa kimanin Mutane dubu 18 ne suka kamu da cutar kwalara A kasar D/Congo daga cikin su 517 sun rasu, domin dakatar da wannan annoba Hukumar ta shirge alurar riga kafi a Kinshasa fadar milkin kasar.
Har ila yau Hukumar ta tabbatar da cewa za ta tura kwararu da kuma kayan aiki domin yakar wannan annobar ta kwalara. baya ga haka hukumar ta yi galgadin kamuwar mutane sama da dubu 300 dake zaune a yankuna masu yawan al'umma na birnin Kinshasa domin hakan ne ma hukumar ta dauki matakin gaggawa na yin allurar riga kafi ga mazauna birnin daga wannan wata na Agusta da muke ciki har zuwa watan Oktoba mai kamawa domin hana wanzuwar wannan annoba.