Shugaban Kasar Gabon ya soki masu sa ido na Kungiyar Turai
Shugaban Kasar Gabon, Ali bongo, ya zargi masu sa ido kan zabe daga kasashen turai da goyon bayan wani bangare, wadanda suka bayyana wasu abubuwa da ke nuna alamun cewa an yi magudi a zaben kasar.
Mista Bongo, ya soki tawagar kungiyar tarayyar turai da ke sanya ido kan zaben kasar, bayan an yi ta ce-ce-ku-ce a kan nasarar da ya yi.
Ya kuma zargi shugaban jam'yyar hamayya Jean Ping da yin magudi.
A ranar Talata ne dai tarayyar turai ta tuhumi sakamakon zaben da aka yi a ranar 27 ga watan Agusta.
A na dai sa ran kotun tsarin mulkin kasar za ta zauna domin sauraren karar da Mista Ping ya shigar a gabanta wanda ke kalubalantar sakamakon zaben.
Mista Bongo ya ce zai bai wa kotun hadin kai idan har ta bukaci a sake kirga kuri'un da aka kada.