Zimbabwe : Kotu Ta Dage Haramcin Zanga-zanga
Kotu a Zimbabwe ta dage dokar hana zanga-zanga da 'yan sanda suka kafa a Harare babban birnin kasar.
A makon jiya ne dai 'yan sanda a kasar suka haramta gudanar da duk wata irin zanga-zanga har tsawan makwanni biyu a birnin na Harare a daidai lokacin 'yan adawa ke gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shugaba Robert Mugabe.
Lauyan 'yan adawan da suka shigar da kara kan haramta masu zanga-zangar, Tendai Biti, ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa '' kotun kolin kasar ta ce hana zanga-zanga baya bisa doka.
Don haka inji Mr Biti lauya kana jagoran jam'iyyar adawa ta PDP yanzu zasu iya ci gaba da gudanar da zanga-zanga.
A kwana baya dai Shugaba Robert Mugabe ya jaddada wajibcin haramta duk wata zanga-zangar 'yan adawa a Harare babban birnin kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawa a wannan kasa suka zazafa zanga-zangar kyammar gwamnatin shugaba Robert Mugabe wace suke zargi da kasawa da kuma jefa kasar cikin mayuyacin hali da tabarbarewar tattalin arziki.
Shugaba Mugabe dai na zargin 'yan adawa kasar da neman wargaza mulkinsa bisa goyan bayan kasashen yamma.