Rikici Ya Barke A Cikin Kungiyar Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10738-rikici_ya_barke_a_cikin_kungiyar_boko_haram
Rahotanni daga Najeriya na cewa rikici ya barke tsakanin 'ya 'yan kungiyar boko haram akan shugabancin kungiyar.
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 07, 2016 12:24 UTC
  • Rikici Ya Barke A Cikin Kungiyar Boko Haram

Rahotanni daga Najeriya na cewa rikici ya barke tsakanin 'ya 'yan kungiyar boko haram akan shugabancin kungiyar.

Mazauna da kuma 'ya 'yan kungiyar sun shaida cewa an shafe makwanni da dama ana gwabza fada tsakanin magoya bayan jagororin kungiyar akan ko wa zai shugabanci kungiyar.

Idan ana tune yau sama da wata guda kenan da kungiyar 'yan ta'ada ta IS da kungiyar boko haram tayi mubayi'a gare ta ta sanar da nada sabon shugaban ta Abou Mosab Al Barnaoui, wanda zai maye gurbin Abubkar Shakau.

Tun dai bayan hakan ne a cewar rahotanni ake gwabza fada tsakanin bangarorin biyu a daidai lokacin da suke shan matsin lamba daga dakarun Najeriya.

Bayanai daga yankin sun ce ko a aranr Alhamis data gabata an kashe mayakan boko haram din dake goyan bayan Shekau a yankin Monguno dake jiyar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wani mazauni yankin ya ce bangaren Al'barnawi sun kai hari ga mayakan Shekau da sukayi kaka-gida a kauyikan Yele da kuma Arafa inda suka kashe da dama daga cikinsu.

A cewar mazamna yankin 'yan bangaren Al'barnaoui na shaida masu cewa mutanen Shekau sun kaucewa hanyar yakin jihadi, inda suka kashe wadanda basuji basu gani ba, kwace dunkiyoyinsu tare da kona gidajensu lamarin da yayi hannu riga da koyarwar addinin musulinci kamar yadda Mele kaka wani mazaunin yankin ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP.