Kasashen Afirka Sun Jaddada Wajabcin Karfafa Aikin Gona
Shugabannin Kasashen Afirka Sun Jaddada Muhammcin Farfado Da Aikin Gona.
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na Kasar Sin, ya nakalto a jiya alhamis cewa; A yayin taron shugabannin Afirka karo na biyu da aka yi a babban birnin kasar Kenya, Nairobi, sun jaddada wajabcin farfado da aikin gona domin samun abinci.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata, da ya gabatar da jawabi a wurin bude taron ya ce; Farfado da aikin gona, wajibi ne domin bunkasa da ci gaban tattalin arziki a rayuwar zamantakewa a cikin nahiyar Afirka.
Shugaban na kasar ta Kenya ya bayyana cewa; Bunkasa Aikin gona zai tabbatar da tsaro ta fuskar abinci a nahiyar sannan kuma zai samar da aikin yi a tsakanin samari maza da mata.
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kigame wanda shi ma ya gabatar da jawabin ya ce; Zuba hannun jari da za a yi a cikin harkokin noma za su daukaka da bunkasa rayuwar mutanen Afirka.