Zaman Lafiya Ya Dawo A Yankin Darfur
Shugaban Kasar Sudan ya ce; Zaman Lafiya Ya Dawo A yankin Darfur.
Shugaban Kasar Sudan ya ce; Zaman Lafiya Ya Dawo A yankin Darfur.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato shugaban kasar ta Sudan "Umar Bashir" yana cewa; Tare da cewa tattaunawa da tarayyar Afirka ta ci tura akan tsagaita wuta a yanin na Darfur, sai dai tun an sami dawowar zaman lafiya ya dawo a yankin."
Umar Hassan al-Bashir ya ci gaba da cewa; Gwamnatin Sudan tana sanar wa dukkanin mazauna Darfur cewa; Gwamnati za ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta.
Har ila yau, shugaban kasar ta Sudan ya ce; Wajibi ne ga kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka domin ganin cewa yarjejeniyar Dauha ta yi nasara, domin ita kadai ne za ta iya warware matsalar yankin Darfur.
Manufar yarjejeniyar ta Dauha dai ita ce kawo karshen yaki tsakanin gwamnatin Sudan da kuma kungiyoyin 'yan tawayen Darfur.
Tun a cikin 2003 ne aka fara rikicin a yankin na Darfur, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka 300,000, ya kuma maida wasu mutane miliyan biyu da rabi zama 'yan gudun hijira.