Adawar Amurka da komawar Riek Machar kan mikaminsa
Amurka ta nuna adawarta da mayar da Riek Machar madugun 'yan tawayen Sudan ta kudu a kan mikaminsa
A yayin wani zaman bayar da bayyanai da yayi tare da 'yan Majalisar kasar sa a wannan Laraba, Donald Booth manzon musamman na kasar Amurka kan kasar Sudan ta Kudu ya bayyana cewa ganin yadda ake ci gaba da tashin hankali a kasar Sudan ta kudu, bai kamata ba Riek Machar madugun 'yan tawayen kasar ya koma kan mikaminsa na mataimakin shugaba na farko a kasar, saboda tun bayan sulhun zaman lafiyar da aka cimma bangarorin biyu ba sa aiki tare domin tabbatar da wannan manufa.
Donald Booth ya ce wannan bayyani da ya yi ba shi ke nufin yana goyon bayan shugaba Salva keiri ba a gudurinsa na wargaza bangaren 'yan adawar kasar ba, saidai ganin cewa bangarorin biyu ba su aiki tare, domin haka ko da Riek Machar ya koma kan mikaminsa nan gaba, kasar na iya komawa gidan jiya.
A shekarar da ta gabata ce Gwamnatin Sudan ta kudu tare da 'yan tawayen kasar suka cimma yarjejjeniyar sulhu, saidai tun ba a je ko ina ba wani sabon rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya tilastawa mataimakin shugaban kasar na farko kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar gudun hijra zuwa kasar Demokaradiyar Kwango.