Gabon : Hankali Ya Karkata Ga Kotun Tsarin Mulki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10804-gabon_hankali_ya_karkata_ga_kotun_tsarin_mulki
A Gabon hankali jama'a kasar ya karkata ga kotun tsarin mulki bayan da bangarorin dake hamaya juna kan sakamakon zaben shugabancin kasar suka shiga kar gaban kotun.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 09, 2016 01:23 UTC
  • Gabon : Hankali Ya Karkata Ga Kotun Tsarin Mulki

A Gabon hankali jama'a kasar ya karkata ga kotun tsarin mulki bayan da bangarorin dake hamaya juna kan sakamakon zaben shugabancin kasar suka shiga kar gaban kotun.

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba da dan takarar 'yan adawa Jean Ping sun kai kara a gaban kotun tsarin mulkin kasar , inda suka zargi juna da tabka magudi a zaben da aka yi a ran 27 ga watan Agusta.

Ali Bongo Ondimba ya kai kara  kan cewa Jean Ping ya tafka magudi sosai a cikin zabe.

A nashi bangare kuwa, Jean Ping ya nuna rashin jin dadi kan sakamakon zabe, kuma ya nemi kotun da ta sake kirga kuri'un da aka kada a garin Bongo wato jihar Haut-Ogooue.

A ran 31 ga watan Agusta hukumar zabe ta kasar Gabon ta bayyana sakamakon zabe cewa, dan takara jam'iyyar Dimokuradiyya kuma shugaba mai ci Ali Bongo Ondimba ya lashe zabe bisa rinjaye kadan.

bayan hakan ne kuma, 'yan adawa magoya bayan jen Ping suka fito zanga-zanga a birnin Libreville hedkwatar kasar inda har ma suka kona majalisar dokokin kasar tare kuma da yin arangama da rundunar tsaron kasar.

Magoya bayan Jean Ping sun sanar da cewa, kuri'un da Jean Ping ya samu ya fi na Bongo yawa, kuma sun ki amincewa da Bongo da ya yi tazarce tare da neman a sake kididdiga kan kuri'u.