MDD ta tura Tawaga ta musamman zuwa kasar Sudan ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10846-mdd_ta_tura_tawaga_ta_musamman_zuwa_kasar_sudan_ta_kudu
Wata Tawaga ta musamman ta MDD ta isa birnin Juba domin gudanar da bincike kan aiki Dakarun wanzar da zaman Lafiya
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 10, 2016 06:39 UTC
  • MDD ta tura Tawaga ta musamman zuwa kasar Sudan ta Kudu

Wata Tawaga ta musamman ta MDD ta isa birnin Juba domin gudanar da bincike kan aiki Dakarun wanzar da zaman Lafiya

Janar "Patrick Camaret", shugaban tawagar musamman ta MDD  ya ce zirayar ta su  na zuwa ne bisa umarnin babban sakatare Janar na MDD Banki Moon domin gudanar da bincike kan zarge -zargen da aka yiwa Dakarun wanzar da Zaman lafiya na Majalisar da ake kira da Minuss.

Janar Patrik Camaret ya kara da cewa bincike kan rawan da Dakarun suka taka a harin da aka kai a Otel Plus shi farko aikin da za su fara a birnin Juba.

A bangare guda, Wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa kazamin rikicin da ya barke a birnin Juba na Sudan ta Kudu a watan Yuli da ya sanya mataimakin shugaban kasa na farko  kuma tsohon jagoran 'yan tawaye Riek Machar ya tsallake daga kasar ,manyan jami'ai na kasar na da masaniya da shi hasali Shugaba Keir da kansa ne ya shirya wannan rikici.