Girgizar Kasa A Kasar Tanzania Ta ci Rayukan Mutane 11
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10855-girgizar_kasa_a_kasar_tanzania_ta_ci_rayukan_mutane_11
A kalla mutane 11 ne su ka kwanta dama sanadiyyar girgizar kasar da ta afku a gunudmar Bokoba da ke arewa maso yammcin kasar Tanzania.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 10, 2016 14:27 UTC
  • Girgizar Kasa A Kasar Tanzania Ta ci Rayukan Mutane 11

A kalla mutane 11 ne su ka kwanta dama sanadiyyar girgizar kasar da ta afku a gunudmar Bokoba da ke arewa maso yammcin kasar Tanzania.

A kalla mutane 11 ne su ka kwanta dama sanadiyyar girgizar kasar da ta afku a gunudmar Bokoba da ke arewa maso yammcin kasar Tanzania.

Babban jami'in 'yansanda a yankin da girgizar kasar ta faru, Augustine Aulomy ya ce; Mun kirga gawawwaki 11 da kuma wadanda su ka jikkata fiye da 100, da aka dauka zuwa asibiti.

Girgizar kasar mai karfi daraja 5,7 a ma'aunin Richard, ta afku ne a kasar ta Tanzania da kuma kasashen da su ke makwabtaka da ita a yau asabar. A kasashen Rwanda da Brundi da Uganda da Kenya an ji girgizar kasar kamar yadda cibiyar da ke kula da girgizar kasa ta Amurka ta bayyana.

Gidaje da gine-gine masu yawa sun zube kasa a garin Bokoba.