Maroko Tana Nan Akan Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki Da Polisario
Moroko Tana Aikin da Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya amabto jakadan Kasar Moroko a Majalalisar Dinkin Duniya, Umar Hilal yana cewa; Kasarsa tana nan akan riko da yarjejeniyar tsagaita wutar yaki da kungiyar Polisario ta yammacin sahara.
Umar Hilal ya ci gaba da cewa; Kasarsa tana cikin shirin ko ta kwana, sai dai tana kai zuciya nesa, sannan kuma tana riko da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Jawabin na Jakadan Moroko a majalisar dinkin duniyar dai ya zo ne adaidai lokacin da ake nuna damuwa akan yiyuwar barkewar rikici tsakanin sojojin kasar da na mayakan kungiyar yammacin sahara ta Polisario.
Tun a 1991 ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bisa shiga tsakanin majalisar dinkin duniya, tsakanin Moroko da mayakan kungiyar ta Polisario. Yarjejeniyar dai ta kawo karshen yakin shekaru 16 a tsakanin bangarorin biyu.