An Fara Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisu A Nijar
An fara gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Jamhuriyar Nijar inda al’ummar kasar za su zabi sabon shugaban kasar cikin 'yan takara 15 da suke fafatawa ciki kuwa har da shugaban kasar mai ci Mahammadu Issoufou wanda ke neman wa'adi na biyu.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Nijar suna nuni da cewa al'amurra suna ci gaba da gudana yadda ya kamata ba tare da faruwar wasu manyan matsaloli ba; kamar yadda kuma bayanai suke nuni da cewa an dau tsauraran matakan tsaro don kare lafiyar al'umma biyo bayan matsalolin tsaro da kasar take fuskanta.
Zaben na yau dai na cike da kalubale da dama bisa la'akari da zargin tafka kura-kurai da aka yi yayin shirya shi sannan kuma ga matsalar tsaro biyo bayan hare-haren ta'addancin kungiyar Boko haram a Kudu Maso Gabashin kasar.
Kimanin mutane miliyan 7 da dubu 500 ne ake sa ran za su jefa kuri'arsu a zaben na yau, inda ake sa ran za a sanar da sakamakonsa kasa da mako guda mai zuwa.