Zimbabwe : Gwamnati Zata Sallami Ma'aikata 25,000
Sep 11, 2016 06:16 UTC
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta kare matakinta na sallamar ma’aikata 25,000 domin ceto kasar daga hanyar tabarbarewar tattalin arziki.
Gwamnatin ta ce zatayi hakan don farfado asusunta dake kan hanyar durkushewa, sai dai ta ce ma'aikatan da za'a kora zasu rika karbar tagomashin albashi na karshen shekara, duk bayan shekaru biyu.
Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin kasar ta fito karara ta bayyana tabarbarewar da tattalin arzikinta ke kan hanya.
Sanarwar tazo bayan da ministan kudin kasar, Patrick Chinamasa ya bayyana cewa albashin ma’aikatan kasar yana lashe kimanin kashi 96% na kasafin kudin gwamnati.
Tags