Paparoma Francis Ya Bukaci Wanzuwar Zaman Lafiya Da Sulhu A Kasar Gabon
(last modified Mon, 12 Sep 2016 03:18:40 GMT )
Sep 12, 2016 03:18 UTC
  • Paparoma Francis Ya Bukaci Wanzuwar Zaman Lafiya Da Sulhu A Kasar Gabon

Shugaban darikar Catholica ta mabiya addinin Kirista ya bukaci al'ummar Gabon da su yi kokarin ganin sun warware rikicin siyasar kasarsu ta hanyar lumana domin samun wanzuwar zaman lafiya da sulhu a kasar.

Shugaban darikar Catholica ta mabiya addinin Kirista Paparoma Francis ya yi kira ga al'ummar Gabon musamman mabiya darikar Catholica da su dauki matakin ganin sun kwadaitar da al'umma kan amfani da salon tattaunawa domin warware dambaruwar siyasar da ta kunno kai a kasar ta hanyar lumana.

Paparoma Francis ya kuma gabatar da addu'a ga ruhin mutanen da suka rasa rayukansu a tarzomar da ta biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Gabon; yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da sulhu a kasar tare da daukan matakin warware sabanin da ya kunno kai ta hanyar lumana.

Tun bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da shugaba Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar da ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata; tarzoma ta kunno kai a kasar sakamakon zargin tafka magudi, inda madugun 'yan adawa Pean Jing yake ganin shi ya lashe zaben kuma tun kafin sanar da sakamakon ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.