'Yan Adawa sun bukaci a gudanar da zanga-zanga a Zimbabwe
Jam'iyun Adawa sun bukaci Al'ummar kasar da su gudanar da zanga-zangar gama gari a Zimbabwe
Kamafanin dillancin labaran Faransa ya nakalto Dougla Mwonzora kakakin 'yan adawa kasar Zimbabwe a jiya Litinin na kiran Al'ummar kasar da su gudanar da zanga-zangar gama gari a fadin kasar gaba daya.
'Yan adawar sun kuduri aniyar ci gaba da gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar, duk kuwa da hani da 'yan sanda suka yi a kasar bayan da suka fitar da wata sabuwar doka wacce ta harmtawa 'yan adawa zanga-zanga a kasar.
A karshen makon da ke tafe ne 'yan adawar ke shirin gudanar da gagarimin gangami domin tilastawa hukumar zaben kasar ta gudanar da wasu gyare gyare kafin gudanar a zabubbukan shekara ta 2018. Jam'iyyu 18 ne dai suka yi gamayyar kyamatar halayyan hukumar zaben da su ke ganin akwai nuna son kai da alamar marawa shugaban kasar Robert Mugabe baya.
Tun bayan da Shugaba Mugabet mai shekaru 92 a Duniya ya bayyana aniyarsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar, masu adawa da shi suka fara gudanar da wannan zanga-zanga.