Mahukuntan Kasar Zimbabwe Sun Saki Wani Jirgin Kasar Amurka Da Suka Kame
Mahukuntan Zimbabwe sun saki wani jirgin daukan kaya mallakin kasar Amurka da ya sauka a cikin kasarsu bayan da suka gano jirgin yana dauke da wasu makuden kudade da gawar wani mutum guda.
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Zimbabwe Charity Charamba ya sanar da manema labarai a jiya Asabar cewa: Bayan gudanar da bincike kan wani jirgin saman daukan kaya mallakin kasar Amurka da ya yi saukan gaggawa a filin jirgin saman birnin Harare fadar mulkin kasar a ranar Lahadin makon da ya gabata, sun kai ga samun tabbacin cewa; Jirgin ya samu matsalar sauka ne a filin jirgin saman Durban na kasar Afrika ta Kudu.
Charamba ya kara da cewa kudaden da suke cikin jirgin mallakin babban bankin kasar Afrika ta Kudu ne kuma a kan doka jirgin ya dauko kudaden, sannan gawar da aka samu a cikin jirgin kayan akwai zaton cewa ta wani mutum ne da ya shiga cikin jirgin ta barauniyar hanya da nufin samun shiga wata kasa ta daban a matsayin bakon haure.