Zimbabwe : An Haramta Zanga Zanga A Harare Har Tsawan Wata Guda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10963-zimbabwe_an_haramta_zanga_zanga_a_harare_har_tsawan_wata_guda
'Yan sanda a Zinbabwe sun haramta gudanar da duk wata irin zanga-zanga ta kyammar gwamnatin shugaba Robert Mugabe a Harare babban birnin kasar har na tsawan wata guda.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 13, 2016 06:41 UTC
  • Zimbabwe : An Haramta Zanga Zanga A Harare Har Tsawan Wata Guda

'Yan sanda a Zinbabwe sun haramta gudanar da duk wata irin zanga-zanga ta kyammar gwamnatin shugaba Robert Mugabe a Harare babban birnin kasar har na tsawan wata guda.

Wannan dokar zata fara aiki daga ranakun 16 ga watan Satumba zuwa 16 ga watan Oktoba mai zuwa.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gamayar jam'iyyun adawa na kasar suka kira wata gagarimar zanga-zanga a ranar Asabar mai zuwa a duk fadin kasar.

Shugaban kasar dai Mugabe dake jagorancin kasar tun a shekara 1980 ya yi alkawarin yuin amfani da karfi domin murkushe duk wata irin zanga-zanga kyammar gwammnatinsa.