Somaliya : Ana Taro Kan Dabarun Yaki Da Al'Shabab
A wani mataki mai nufin lalubo hanyoyin kara karfin yakar mayakan Al-Shabaab, sojoji injiniya daga MDD da kungiyar tarayyar Afirka(AU) na wani taron karawa juna sani a birnin Mogadisho na kasar Somaliya.
Taron dai ya hada injiniyoyi daga tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka (AMISON), da Biritaniya, da ofishin ba da tallafi na MDD da ke kasar Somaliya (UNSOS).
A jawabinsa na bude taron na yini biyu a jiya Litinin, wakilin musamman na shugabar hukumar zartarwar kungiyar AU da ke Somaliya, Jakada Francisco, ya yi kira da a yi wa ayyukan injiniya gyaran fuska ta yadda tawagar AMISON zata yaki kungiyar Al-Shabaab.
Rawar da sojojin injiniya za su taka, ta hada da tsara gine-gine, girka na'urori, kula da zirga-zirgar dakaru, tabbatar da tsaro, daura damara da sauran muhimman rawar da ake bukata su taka a fagen daga.