Boko Haram Ta Ce Zata Cafke Shugaban Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11032-boko_haram_ta_ce_zata_cafke_shugaban_najeriya
A wani sabon faifan bidiyo data fitar kungiyar Boko Haram ta ce za ta cafke shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 14, 2016 06:23 UTC
  • Boko Haram Ta Ce Zata Cafke Shugaban Najeriya

A wani sabon faifan bidiyo data fitar kungiyar Boko Haram ta ce za ta cafke shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Bidiyon na mintina 13 wanda aka dauka a wani boyayyen wuri ya nuna mayakan na gudanar da sallar idin babba sallah a ranar litinin data gabata. 

Kungiyar a karkashin jagorancin Abubakar Shekau ta ce, da yardan Allah za ta kama shugaba Buhari wanda ta bayyana shi a matsayin kafiri da hannunta.

Sai dai a wannan karon ma, jagoran  kungiyar, Abubakar Shekau bai bayyana a cikin bidiyon ba in da mataimakinsa ya isar da sakon.