Zanga-zangar goyon bayan Shugaba Ali Bango A Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11080-zanga_zangar_goyon_bayan_shugaba_ali_bango_a_gabon
Duban magoya bayan Shugaba mai ci Ali Bango na kasar Gabon sun gudanar da zanga-zangar goyon baya a birnin Libreville.
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 15, 2016 10:43 UTC
  • Zanga-zangar goyon bayan Shugaba Ali Bango A Gabon

Duban magoya bayan Shugaba mai ci Ali Bango na kasar Gabon sun gudanar da zanga-zangar goyon baya a birnin Libreville.

kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa a jiya laraba duban magoya bayan shugaba Ali Bongo Ondimba sun gudanar da zanga-zanga lumana domin nuna goyon bayan su shugaban a birnin Libreville fadar milkin kasar. mahalarta zanga-zangar na dauke da kyalaye da aka zana hoton Shugaban kasar ta Gabon Ali Bongo Ondimba tare da rera taken yin Allawadai da tashin hankali da ya faru bayan zaben, har ila yau mahalarta zanga-zangar na rera taken kiyayya ga Madugun 'yan adawar da ya sha kayi a zaben shugaban kasar da ya gabata, inda suke cewa ba ma kaunar Jean Ping sai Ali Bongo zabebben shugaban kasar ta hanyar Demokaradiya.

Rahoton ya ce an gudanar da zanga-zangar cikin kwararen matakan tsaro da ta dauki tsahon sa'a guda ana gudanar da ita.wannan zanga-zanga na zuwa ne a yayin da dan Takarar 'yan adawa Jean Ping ya shigar da kara na kalubalantar zaben a gaban kotun tsarin milkin kasar inda ya bukaci da a sake girka kuri'un da aka kada a a yankin Haut-Ogooue inda aka ce shugaba Bongon ya sami kashi 95 cikin dari na kuri'un da aka kada inda aka ce kashi 99.9 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a sun fito zaben.

Sanar da sakamakon zaben dai yayi sanadiyyar barkewar rikici inda alal akalla mutane 6 suka mutu da kuma kame wasu kimanin dubu guda.