An Hallaka Kwamandodin Boko Haram 4 A jihar Yobe
Majiyar tsaron Najeriya ta sanar da hallaka Kwamandodin boko haram 4 a kauyen Djourou na jihar Yobe dake shiyar arewa maso gabashin kasar
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alkhamis Majiyar ta ce Sojoji tare da 'yan kato da gora sun kai harin bazata a wurin taruwar mayakan kungiyar Boko haram dake kauyen Djourou, inda suka samu nasarar hallaka Kwamandodin boko haram din guda 4 tare da kame wani guda na daban daga cikin su.
Majiyar tsaron ta ce babu wani soji ko kuma dan kato da gora da ya rasa ransa ko kuma ya jikkata.Rahoton ya kara da cewa Sojoji kasa da na sama na Kasar na ci gaba da kokari wajen kai hare-hare kan maboyar 'yan boko haram din domin kakkabe su daga cikin kasar gaba daya.
Tun daga shekarar 2009 ne kasar ta Najeriya ta fara fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko haram a shiyar arewa maso gashin kasar, alkaluma sun ce daga wannan lokacin zuwa yanzu sama da Mutane dubu 20 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu miliyon biyu da dubu 600 suka yi gudun hijra sanadiyar rikicin na Boko Haram.