An kawo karshen taron kungiyar IGAD a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11089-an_kawo_karshen_taron_kungiyar_igad_a_somaliya
Kungiyar Kungiyar Bunkasa tattalin arzikin gabashin Afikra ta kawo karshen zaman ta a birnin Magadushu na kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T11:28:56+00:00 )
Sep 15, 2016 17:46 UTC
  • An kawo karshen taron kungiyar IGAD a Somaliya

Kungiyar Kungiyar Bunkasa tattalin arzikin gabashin Afikra ta kawo karshen zaman ta a birnin Magadushu na kasar Somaliya

Taron wanda aka fara tun daga ranar Talatar da ta gabata, a kawo karshen sa a wannan Alkhamis, inda a karshen taron aka jajjada tabbatar da tsaro tare da gudanar da zabe a kasar ta Somaliya.

Rahoton ya ce a yayin zama an tabka mahawura dangane da yadda za a gudanar da zabe a kasar Somaliyan a lokacin da aka yanke da kuma yadda za a karfafa matakan tsaro a yayin gudanar da zaben ko baya ga hakan taron ya tattauna kan yanayin siyasar da yankin ke ciki.

Kungiyar ta IGAD ta kumshi kasashen Djibouti, Ethiopia, Eritria, Kenya, Sudan ta kudu, Sudan, Somaliya gami da Uganda kuma wannan shi ne karo na 53 da kungiyar da kungiyar ta gudanar ta.

A bangare guda Francisco Madeira Manzon musaman na kungiyar Tarayyar Afirka a Somaliya ya tabbatar da gudanar da zaben Somaliyan a ranar 30 ga watan Oktoba mai kamawa.