Zaman Taron Shugabannin Kasashen Yankin Gabashin Afrika A Kasar Somaliya
Jawabin bayan taron shugabannin kasashen yankin gabashin Afrika ya bukaci gudanar da ingantaccen zabe cikin adalci a kasar Somaliya tare da hanzarta kawo karshen dambaruwar siyasar kasar Sudan ta Kudu.
Shugabannin kasashen yankin gabashin Afrika mambobi a kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yankin gabashin Afrika ta IGAD a karon farko a cikin shekaru 30 da suka gabata sun gudanar da zaman taro a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya, inda aka bude zaman taron a ranar Talata 13 ga watan Satumban da muke ciki kuma zaman taron ya zo karshe a jiya Alhamis 15 ga watan na Satumba.
Zaman taron shugabannin kasashen kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin yankin gabashin Afrika ta IGAD karo na 28 ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasashen yankin musamman irin gagarumin ci gaban da aka samu ne a fagen siyasa da tsaro a kasar Somaliya tare da gabatar da shawarwari kan neman hanyar warware dambaruwar siyasar Sudan ta Kudu da ta wurga kasar cikin yakin basasa. Kasashen yankin gabashin Afrika mambobi a kungiyar IGAD sun hada da Kenya, Habasha, Djibouti, Eritiriya, Sudan, SUdan ta Kudu, Somaliya da kuma Uganda.
Mahalarta zaman taron sun tattauna batun hanyar da za a bi na ganin an gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun Dokoki a Somaliya cikin kwanciyar hankali tare da karfafa matakan tsaro a lokacin zabukan gami da hanyoyin da za a bi wajen ganin dakarun wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa na AMISOM da sojojin gwamnatin Somaliya sun samu nasarar 'yantar da dukkanin yankunan Somaliya daga mamayar mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shahab.
Masharhanta sun bayyana wannan zaman taro na shugabannin kasashen kungiyar IGAD da aka gudanar a kasar Somaliya da ta kwashe tsawon shekaru kimanin 26 tana fama da matsalar yakin basasa; a matsayin wani babban sako ga duniya cewa; Somaliya ta kama hanyar samun zaman lafiya sakamakon nasarar da sojojin gwamnatin kasar da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa na AMISOM suke samu a kan mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.