An Kame Masu Fafutukar Kare Demokradiyya 16 A Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11122-an_kame_masu_fafutukar_kare_demokradiyya_16_a_kasar_jamhuriyar_demokradiyyar_congo.
A yau juma'a jami'an tsaron kasar Demokradiyyar Congo Sun kame masu fafutukar kare demokradiyya 16
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 16, 2016 14:24 UTC
  • An Kame Masu Fafutukar Kare Demokradiyya 16 A Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

A yau juma'a jami'an tsaron kasar Demokradiyyar Congo Sun kame masu fafutukar kare demokradiyya 16

Majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta ce; a yau juma'a jami'an tsaron kasar Demokradiyyar Congo Sun kame masu fafutukar kare demokradiyya 16.

Majiyar ta ce; An kame mutanan ne dai a lokacin da su ke yin taro domin tattauna yadda za su hana shugaba Joseph Kabila tsawaita lokacin mulkinsa da ya sabawa doka.

Jami'i mai kula da kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya Jose Maria Aranaz da ya bada labarin ya kuma kara da cewa; an kame mutanan ne da su ke taron yin kira da a girmama kundin tsarin mulki.

Sai dai kakakin gwamnatin kasar Lambert Mende ya bayyana mamakinsa akan zargin da ake yi wa gwamnati.