Kungiyar Ashabab ta kwace wani gari a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11146-kungiyar_ashabab_ta_kwace_wani_gari_a_somaliya
Kungiyar Ashabab ta kwace garin Elwak na kasar Somaliya dake kusa da iyaka da kasar Kenya a jiya Juma'a
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 17, 2016 01:20 UTC
  • Kungiyar Ashabab ta kwace wani gari a Somaliya

Kungiyar Ashabab ta kwace garin Elwak na kasar Somaliya dake kusa da iyaka da kasar Kenya a jiya Juma'a

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Magadushu ya nakalto Abdulkadir Alami daya daga cikin Jami'an tsaron Somaliya na cewa a marecen jiya Juma'a mayakan kungiyar Ashabab sun kai farmaki garin Elwak inda suka kashe Sojoji akalla 12,tare kuma da mamaye garin bayan da Dakarun tsaron dake cikin garin suka ja baya.

A nata bangare Kungiyar Ashabab din a cikin shafinta na yanar gizo ta wallafa labarin cewa ta kai farmaki garin Elwak dake kusa da iyakar kasar da kasar Kenya sannan ta kashe sojoji masu yawa tare da samun nasarar kwace iko da gari.

kimanin shekaru biyar kenan da aka fatattaki mayakan kungiyar Ashabab  daga birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya da wasu manyan buraren kasar, amma tun daga wannan lokaci zuwa yanzu mayakan na Ashabab na ci gaba da kai hare-hare kan Gwamnatin dake samun goyon bayan kungiyoyin kasa da kasa.