'Yan Sandan Zimbabwe Sun Shirya Fada Da Masu Adawa Da Gwamnatin Kasar
Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun bayyana cewar 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar na cikin shirin ko ta kwana don fada da abin da suka kira 'duk wani kokarin karya dokokin kasar da kuma gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewa bisa a makon da ya wuce ne 'yan sandan kasar Zimbabwen suna sanar da cewa daga ranar Asabar din nan (wato yau kenan) an haramta gudanar da wata zanga-zanga a birnin Harare babban birnin kasar, don haka za su yi fada duk wani da ya karya wannan doka.
Rahotannin sun ce rundunar 'yan sandan kasar sun sanar da cewa 'yan sandan kwantar da tarzoma suna cikin shirin ko ta kwana don fada da duk wani kokari na gudanar da zanga-zangar biyo bayan kokarin 'yan adawan kasar na gudanar da zanga-zangar kin jinin shugaba Mugaben.
'Yan adawan dai sun ce ba su amince da wannan doka ta 'yan sandan ba kuma za su kalubalance ta a kotu.