Somaliya : An Kwato Garin Elwak Daga Hannun Al'Shabab
Rahotanni daga Somaliya na cewa hadin gwiwar sojojin kasar da rundinar kiyaye zamen lafiya ta kungiyar tarayya Afrika wato (Amisom) sun karbe ikon garin Elwak dake kan iyaka kasar da Kenya daga hannun mayakan Al'Shabab.
Mjiyoyin gwamnati a yankin sun ce hadin gwiwar dakaraun sun kwace daukacin ikon garin da mayakan na Al'shabab suka kwace ikonsa a jiya Juma'a.
Kwamishinan 'yankin na Elwak Ibrahim Guled, ya shaidawa masu aiko da rahotannin cewa mayakan na Al'shabab sun arce daga garin a wannan Asabar dama suka samu labarin zuwan dakarun.
Saidai a cewar wani mazaunin yankin mayakan sun tsere tun cikin daren jiya bayan da suka kwashi ganima a barikin sojin yankin.
Hukumomin yankin dai sun ce sojojin kasar shida ne suka rasa rayukan su a yayin fadan da aka kwashe kusan sa'a kuda ana gwabzawa da 'yan Al'shabab din da suka shigo garin a jiya Juma'a cikin motocin sojin kasar Kenya.