Sudan Ta Yi Barazanar Rufe Kan Iyakokinta Da Sudan Ta Kudu
Gwamnatin Sudan ta yi barazanar rufe kan iyakanta da kasar Sudan ta Kudu cikin kwanaki masu zuwa matukar dai makwabciyar nata ba ta kori kungiyoyi masu dauke da makamai da suke cikin kasar ba.
Karamin ministan harkokin wajen kasar ta Sudan Kamal Isma'il ne ya shaida wa kafafen watsa labaran gwamnatin kasar hakan inda ya ce wajibi ne gwamnatin Sudan ta Kudun ta kori 'yan kungiyoyi masu dauke da makami da suke kai hare-hare kan wasu yankuna na kasar Sudan din da suka hada da Darfur, Blue Nile da kuma Kudancin Kordofan.
Ministan ya kara da cewa mahukutan a Sudan ta Kudun sun yi alkawarin korar masu dauke da makamin cikin kwanaki 21 a ziyarar da ya kai can a kwanakin baya. Don haka ya ce gwamnatinsu za ta rufe kan iyakar matukar dai Sudan ta Kudun ba ta cika alkawarin da ta dauka ba.
Gwamnatin Sudan din ta jima tana zargin gwamnatin Sudan ta Kudun da goyon bayan masu dauke da makamin.