Kungiyar Boko Haram ta kai Coci a Najeriya
Akalla Mutane takwas suka rasu sanadiyar harin ba zata da mayakan Boko Haram suka kai a Cocin Kwamjilari, na jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya
Kamfanin dillancin labaran France Press ya habarta cewa mayakan kungiyar Boko Haram bisa babura sun kai wani harin bazatana kan mabiya Addinin kirista na kauyen Kwamjilari,dake jihar Borno, a yayin da suka kamala ibadar su da suka saba a ko wata ranar Lahadi,inda suka bude musu wuta sannan kuma suka tsinna wuta a cocin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane takwas.
Kafin wannan Hari, kungiyar Boko haram din ta dauki alhakin harin da aka kai a wasu coci biyu dake kusa da wannan kauye lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane uku.
Kimanin shekaru bakwai kenan da Kasar Najeriyan ke fuskantar hare-haren ta'adancin kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya lashe rayukan Mutane kimanin dubu 20 da kuma hijra na Mutane kimanin million biyu da dubu 600.