MDD ta yi gargadin karamcin Abinci a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11332-mdd_ta_yi_gargadin_karamcin_abinci_a_somaliya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashin 40% na Al'ummar Somaliya na fuskantar yinwa
(last modified 2018-08-22T06:58:57+00:00 )
Sep 21, 2016 02:50 UTC
  • MDD ta yi gargadin karamcin Abinci a Somaliya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashin 40% na Al'ummar Somaliya na fuskantar yinwa

A wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan talata, kimanin Mutane miliyan biyar ne daga cikin Al'ummar kasar Somaliya ba su da isashen abinci, kuma idan aka yi la'akari da rahoton karshe na Majalisar da ta fitar a watan favrayun da ya gabata adadin ya karu da sama da dubu 300.

Rahoton ya ce a halin da ake cikin sama da Mutane miliyan guda da dubu 100 ne na al'ummar kasar Somaliya ba sa iya samun abinci da za su ci a yini, kuma wasu miliyan uku da dubu 900 na daban suna bukatar agaji domin ci gaba da rayuwa.

Majalisar ta kara da cewa daga cikin wannan adadi sama da dubu 300 kananen yara 'yan kasa da shekaru biyar kuma dubu 50 daga cikin su suna cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai.

 Har ila yau Majalisar ta kara da cewa halin da 'yan kasar Somaliyan suka tsinci kansu ciki abin tashin hankali ne duba da yadda a yanzu duniya ke fama da matsaloli na fari da ambaliyar ruwa da rikice-rikice ga karuwar 'yan gudun hijira.

Dubban 'yan gudun hijira ne cikin wannan shekara sun koma kasar ta Somaliya daga sansanin Dadaab, bayan da kasar Kenya ta bayyana shirin rufe sansani baki daya a watan Nuwamba.