A kwato Garin Malam Fatori daga hannun Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11335-a_kwato_garin_malam_fatori_daga_hannun_boko_haram
Rundunar hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi sun kwato garin Malam Fatori a arewacin jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram
(last modified 2018-08-22T06:58:57+00:00 )
Sep 21, 2016 02:56 UTC
  • A kwato Garin Malam Fatori daga hannun Boko Haram

Rundunar hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi sun kwato garin Malam Fatori a arewacin jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram

A wata sanarwa da mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar sojan Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar ta ce Rundunar hadin gwiwar sun yi  amfani da sojojin kasa da kuma jiragen yaki wajen fatattakar 'yan Boko Haram daga cikin garin, tare da hallaka mayakan na boko haram da dama

Kukasheka ya shedawa manema labarai cewa a baya mayakan na Boko Haram  sun kai wa sojojin rundunar tsaron hadin gwiwa hari a garin, amarin da ya tilastawa Sojoin ja da baya

Sanarwa ta ce babu wani soji da ya rasa ransa ko kuma ya jikkata a yayin kai harin

Malam Fatori dai shi ne gari mafi girma a karamar hukumar Abadam dake jihar Borno dake kan iyaka da jumhoriyar Nijer kuma a cikin sa a kwai dubban 'yan gudun hijira da suka samu mafuka.