Damuwar Kungiyar AU kan halin da Kasar D/Kwango ke ciki
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana damuwar ta kan halin da Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango ke ciki
A wata sanarwa da ta fitar, Shugabar Kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Nkosazana Dlamani Zuma ta bayyana damuwar ta kan abinda ya faru a yayin da 'yan adawa suka gudanar da zanga-zanga a kasar Demokaradiyar Kwango.
Shugabar ta bukaci Gwamnati da ta tattauna da 'yan adawa domin samar da maslaha na yadda za a gudanar da zabe mai zabta a kasar, inda ta bayyana cewa wannan ita ce hanya daya cilo na samun mafuta a kasar.har ila yau sanarwar ta kara da cewa Kungiyar na bin dindigin abinda ke gudana a kasar ta Kwango domin haka tana karfafa bangarorin biyu da su zauna kan tebirin shawara domin kalubalantar duk wani tashin hankali a nan gaba.
A watan Nuwanbar wannan shekara ne aka shirga za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Kwango, amma saboda rashin shiri, hukumar zaben ta dage shi zuwa wani lokaci na daban, to saidai 'yan adawa sun zarki Shugaban kasar da yin hakan domin ya ci gaba da zama a kan karagar milkin kasar.