RDC : Kura Ta Lafa A Kinshasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11371-rdc_kura_ta_lafa_a_kinshasa
Rahotanni daga Jamhuriya demukuradiyyar Congo na cewa kura ta lafa a Kinshasa babban birnin kasar, bayan kwashe kwanaki biyu ana dauki- ba- dadi tsakanin jami'an tsaro da matasa dake zanga-zanga kyammar mulkin Shugaba Joseph Kabila.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 21, 2016 14:17 UTC
  • birnin Kinshasa na RDC
    birnin Kinshasa na RDC

Rahotanni daga Jamhuriya demukuradiyyar Congo na cewa kura ta lafa a Kinshasa babban birnin kasar, bayan kwashe kwanaki biyu ana dauki- ba- dadi tsakanin jami'an tsaro da matasa dake zanga-zanga kyammar mulkin Shugaba Joseph Kabila.

Kawo yanzu dai hukumar 'yan sanda ta kasar ta ce adaddin wucin gadi na mutanen da suka mutu ya kai 32, da suka hada da jami'an tsaro da kuma fararen hula.

Tashin hankalin da aka gani tsakanin ranakun Litinin zuwa talata shi ne irinsa mafi muni da kasar ta fuskanta tun farkon wannan shekara.

Rikicin dai ya barke ne a farkon wannan mako a lokacin zanga-zanga da 'yan adawa na kasar suka shirya watannin uku gabanin karshen wa'adin mulkin shugaban kasar Joseh Kabila dake karewa a ranar 20 ga watan Disamba domin yi masa kashedi akan sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar.

Kundin tsarin mulkin kasar dai ya haramtawa Mista kabila dake shugabancin kasar tun cikin shekara 2001 sake tsayawa takara, saidai a cewar 'yan adawan har yanzu Mr. Kabila nada kwadayin sake tsayawa takara.