Akwai Fatan Za'a Sami Tabbataccen Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11386-akwai_fatan_za'a_sami_tabbataccen_zaman_lafiya_a_sudan_ta_kudu
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa akwai fatan za'a sami tabbataccen zaman lafiya idan an aiwatar da yerjejeniyar da aka cimma tsakaninta da banagren yan tawaye.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 22, 2016 04:14 UTC
  • Akwai Fatan Za'a Sami Tabbataccen Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayyana cewa akwai fatan za'a sami tabbataccen zaman lafiya idan an aiwatar da yerjejeniyar da aka cimma tsakaninta da banagren yan tawaye.

Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto mataimakin shugaban kasar Sudan James Wani Igga yana fadar haka a jiya Laraba 21 ga watan Satumba, a taron bukin ranar sulhu ta duniya ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don wayar da kan mutanen duniya dangane da sulhuntawa a tsakaninsu musamman a kasashen da ake yake yake ko kuma suke fama da rigingimu.

Igga ya kara da cewa abu mafi muhimmanci wanda kasar Sudan ta kudu take bukata a halin yanzu shi ne samar da zaman lafiya a cikin kasar, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar tana iya kokarinta don ganin an aiwatar da yerjejeniyar sulhun ta ta cimma tare da yan tawaye wanda ta wannan hanyar kadai kasar zata zauna lafiya sannan ta ci gaba.

Tun cikin watan Decemban shekar ta 2013 ne kasar Sudan ta kudu ta fada cikin yakin cikin gida tskanin gwamnatin shugaba Silva Kiir da tsaohon mataimakinsa Reak Macher. Rikici wanda ya lashe dubban rayukan mutanen kasar da kuma maida wasu miliyoyi yan gudun hijira.