Zanga-zangar Neman Sakin Sheik Zakzaky A Abuja
Dalibai Sun gudanar da zanga-zangar neman a saki Sheikh Zakzaky A Abuja.
Kungiyar "Yan'uwa Musulmi a Najeriya ta gudanar da Zanga-zangar neman a saki Sheik Ibrahim Zakzaky a birnin Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarun Rasa ya ambato cewa; Daruruwan 'yan kungiyar ta "Harkar Musulunci A Najeriya ne su ka yi zanga-zangar a birnin Abuja tare da neman a saki Sheikh Ibrahim alzakzaky ba tare da wani sharadi ba.
A bayanin da masu Zanga-zangar su ka fitar sun yi tir da kisan da sojojin su ka yi a Zaria tare kuma da yin kira a kawo karshen yadda ake cutar da 'yan shi'ar kasar.
Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake wajen tarwatsa zanga-zangar ta lumana, kamar kuma yadda su ka kama wasu.