Mayakan Ashabab sun kai hari kan 'yan sanda a Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11440-mayakan_ashabab_sun_kai_hari_kan_'yan_sanda_a_kenya
Jami'an 'yan sandar Kenya sun sanar da harin da aka kaiwa wani sansanin su dake kan iyakar kasar da Somaliya
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 23, 2016 02:22 UTC
  • Mayakan Ashabab sun kai hari kan 'yan sanda a Kenya

Jami'an 'yan sandar Kenya sun sanar da harin da aka kaiwa wani sansanin su dake kan iyakar kasar da Somaliya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto George Kinoti kakakin 'yan sandar kasar Kenya na cewa harin an kai shi ne a sansanin 'yan sanda dake yankin Hamey na garin Liboi dake arewa maso gabashin kasar kusa da kan iyakar kasar Somaliya, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar 'yan sanda 4 daya daga cikin su na cikin mawuyacin hali.

A nata bangare, kungiyar ta Ashabab ta tabbatar da kai harin, inda ta ce ta hallaka Jami'an 'yan sandar kenyar  akalla guda 6 sannan kuma ta yi awan gaba da wasu  biyu na daban.

Wannan hari na zuwa ne a yayin da kasar ke jimamin tuni da zagayowar harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kai a cibiyar kasuwancin nan ta Westgate dake birnin Nairobi shekaru uku da suka gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 67.