Zaben Gabon : Zaman Dar-dar Gabanin Hukuncin Kotu
A kasar Gabon yau Juma'a ne ake dakon hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar zata yanke kan jayayyar dake tsakanin shugaba mai barin gado, Ali Bongo Ondimba, da abokin hamayyarsa, Jean Ping, akan sakamakon zaben shugaban kasar daya bar baya da kura.
Saidai rahotanni daga wannan kasa na cewa jama'a na cikin zaman dar-dar kasancewar ba'a san abinda zai biyo bayan hukuncin ba, duba da irin tashin hankula da aka gani a makwanin baya, jin kadan bayan sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Agusta, wanda kuma hukumar zaben kasar ta ce Ali bango ne yayi nasara.
Babban aikin dake gaban kotun tsarin mulkin kasar shi ne tabbatar cewa ko lalle Ali Bango shugaban kasar mai ci ya lashe zaben ko kuma A'a.
Abubuwa biyu ne zasu iya fitowa a hukuncin, ko kutun ta amunce da zaben Ali Bango ko kuma tayi wasti da sakamakon zaben, wanda kuma zai baiwa abokin hamayyarsa Jean Ping daya bayyana kansa a matsayin zababen shugaban kasar gaskia akan karar daya shigar..
Dan takarar shugabancin kasar ne na jam’iyar adawa da ya sha kayi a zaben da aka gudanar, ya shigar da kara a gaban kotun tsarin mulki don kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa shugaba mai ci Ali Bongo Odimba nasara.
Mista Ping ya shigar da kara ne akan a sake kirga kuri'un da aka kada musamen a yankin ''Haut-Ogooué'' mahaifar shugaban kasar inda Ali Bango din ya samu kashi 95% na yawan kuri'un da aka kada.
Kotun tsarin mulkin kasar dai ta shafe makwanni biyu kafin ta yanke hukunci kan karar da Jean Ping ya shigar in da daga nan ne ta shiga aikin sake kirga kuri'un da aka kada domin tabbatar da hakikanin wa yayi nasara a zaben wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen kasar.
Kotun dai ta kunshi alkalai tara, da masu taimaka masu na kungiyar tarraya Afrika da suka hada da shugaban kotun tsarin mulkin kasar Chadi da wani mamba na kotun tsarin mulkin kasar Togo da kuma masu sa ido na kasashen waje.
An samu barkewar rikice-rikice a wasu biranen kasar bayan da hukuamar zabe ta sanar da sakamakon, abinda ya haddasa asarar rayuka da dama, hakan ne kuma yasa a yau al'ummar ke cikin fargaba akan abunda zai iya biyo bayan hukuncin da ake sa ran kotun zata yanke a yau Juma'a, koda yake wasu rahotanni na cewa mai yiwa ne ma kotun ba zata iya yanke hukunci a yau ba.
Tazarar kuri’u dubu sittin ne a tsakanin Ali Bongo da Ping kamar yadda sakamakon zaben na ranar 27 ga watan Augusta ya nuna.
Wa'adin kwanaki 15 dai shi ne kundin tsarin mulkin wannan kasar ya tanada, muddun dai wani dan takara ya garzaya kotu akan cewa ba'a masa adalci ba a zabe.
Saidai fa wani abu dake daukan hankali kamar yadda rahotanni suka ambato shi ne yadda tun a yammacin jiya aka jibge jami'an tsaro tare da takaita zirga-zirga a titunan dake kaiwa kotun a Libreville babban birnin kasar.
Wannan kuwa yana nuna yadda kotun ke fargabar abunda zai iya biyo baya a hukukunci da zata yanke, musamen idan ta bayyana Shugaban kasar mai ci Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben.
Dama kafin hakan akwai ministocin da suka ja kunnan abokin hammayar shugaban kasar, wato Jean Ping da cewa idan har ya wuce gona da iri kuma bai samu nasara ba a karar daya shigar, to zasu garkame shi a gidan kaso.
A yanzu dai makomar kasar na ga hannun shugabar kotun tsarin mulkin kasar, Marie-Madeleine Mborantsuo, wace ta bukaci ga masu gabatar da kara dasu sanarwa da lauyoyin bangarorin biyu rana da kuma lokacin da za'a sanar da hukuncin kotun.