Tashe-Tashen Hankula Suna Ci Gaba Da Yin Kamari A Kasar Gabon
Ana ci gaba da samun bullar tashe-tashen hankula a kasar Gabon duk da cewa ana zaman jiran hukuncin da kotun kundin tsarin mulkin kasar zata fitar kan sakamakon zaben shugaban kasa da ake ci gaba da samun takaddama a kai.
Tun bayan da madugun 'yan adawa a Gabon Jean Ping ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar a cikin watan Agustan da ya gabata, rikici ya kunno kai a kasar lamarin da ya kai ga samun hasarar rayuka da na dukiyoyi.
Madugun 'yan adawar Jean Ping a karshe ya shigar da kara a gaban kotun kundin tsarin mulkin kasar, inda a halin yanzu ake zaman jiran hukuncin da zata gabatar kan sakamakon zaben, amma duk da haka ana ci gaba da samun bullar tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar.
Hukumar zaben kasar Gabon dai ta sanar da cewa: Shugaba Ali Bango ne ya lashe zaben da kashi 49 cikin dari, yayin da madugun 'yan adawar kasar Jean Ping ke biye masa da kashi 48 cikin dari.