Kotun Kolin Kasar Gabon ta tabbatar da ingancin zaben shugaban kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11476-kotun_kolin_kasar_gabon_ta_tabbatar_da_ingancin_zaben_shugaban_kasa
Tashar telbijin din Farance 24 ta ce; Kotun tsarin mulkin kasar Gabon ta bayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zabe.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 24, 2016 04:49 UTC
  • Kotun Kolin Kasar Gabon ta tabbatar da ingancin zaben shugaban kasa

Tashar telbijin din Farance 24 ta ce; Kotun tsarin mulkin kasar Gabon ta bayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zabe.

A jiya juma'a ne dai kotun kolin kasar ta Gabon ta bayyana Ali Bongo Ondimba da cewa shi ne wanda ya ci zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 27 ga watan Augusta.

Bugu da kari, kotun ta yi watsi da karar da abokin hamayyar Bongo Jean Ping ya shigar akan zaben. Har ila yau, kotun ta ce; bukatar a sake kidaya kuri'un da aka kada, a yayin zaben, ba abu ne mai yiyuwa ba.

Ali Bongo zai sake yin wani sabon zango na shugabancin kasar ta Gabon na shekaru bakwai.

Bayan sanar da sakamakon zaben dai an sami rikici a kasar ta Gabon wanda ya haddasa asarar rayuka da ta dukiya da kuma jikkata da dama.