Sudan Ta Kudu Ta Bayyana Damuwarta Kan Shirin Kakaba Mata Takunkumin Makamai
Sep 24, 2016 07:45 UTC
Sabon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu ya bayyana damuwar kasarsa kan shirin kakaba mata takunkumin sayar da makamai.
A jawabinsa ga manema labarai a harabar majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma'a: Sabon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Taban Deng Gai ya bukaci cewa kada a yi saurin daukan matakin kakaba wa kasarsa takunkumi, domin a halin yanzu Sudan ta Kudu ta kama hanyar samun wanzuwar zaman lafiya da sulhu bayan shekaru biyu da rabi tana fama da matsalolin tashe-tashen hankula.
Kasar Amurka dai ta yi barazanar kakaba wa Sudan ta Kudu takunkumin hana sayar mata da makamai matukar gwamnatin kasar ta ki amincewa da shirin tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa cikin kasar.
Tags