Jami'an Tsaron Gabon Sun Kame Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11497-jami'an_tsaron_gabon_sun_kame_tsohon_shugaban_hukumar_leken_asirin_kasar
Jami'an tsaron Gabon sun kame tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar kan zargin hannu a kara ruruta wutan rikicin siyasa a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 24, 2016 07:47 UTC
  • Jami'an Tsaron Gabon Sun Kame Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin Kasar

Jami'an tsaron Gabon sun kame tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar kan zargin hannu a kara ruruta wutan rikicin siyasa a kasar.

Tashar talabijin ta kasar Faransa ta "France 24" ta watsa rahoton cewe: Jami'an tsaron Gabon sun kai samame gidan tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Leon Paul Ngoulakia a birnin Libreville fadar mulkin kasar, inda suka yi awungaba da shi kan zargin hannu a kara ruruta wutan rikicin siyasa a kasar da ta kunno kai tun bayan sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar.

Leon Paul Ngoulakia ya kasance daga cikin magoya bayan shugaba Umar bango amma daga baya ya canja sheka zuwa bangaren 'yan adawa da suke kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar a cikin watan Agustan wannan shekara.

A gefe guda kuma kotun kula da kundin tsarin mulkin kasar Gabon a jiya Juma'a ta sanar da sahihancin zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata da ya kai ga nasarar shugaba mai ci a kasar Umar Bango, wannan sanarwa ta zo ne a matsayin hukuncinta kan karar da madugun 'yan adawar kasar Jean Ping ya shigar gabanta yana kalubalantar ingancin zaben saboda zargin tafka magudi.