Mayakan Bakasi A Jihar Rivers Ta Nigeria Sun Kashe Sojojin Gwamnati Biyu
Sojojin Nigeria biyu ne suka mutu a wani harin da ake zaton mayakan Niger Dalter ne suka kai masu a safiyar yau Asabar a karamar hukumar Bakasi na jihar Rivers.
Jaridar Sahara Reporter ta yanar gizo ta nakalto kakakin sojojin Nigeria na riko Kanar Sabi K Usman yana fadar haka bayan harin a safiyar yau ya kuma dora laifin kan wasu tsageru wadanda sojojin suke nemansu, karkashin shugabncin wani mai suna Benjamin Simplee . Usman ya kara da cewa maharan sun zo cikin wani jirgin ruwa mai tsananin gudu suka bude wutan kan sojojin Nigeri, bayan kisan sojojin biyu, wasu biyu ma su bace amma daga baya an ganosu.
Majiyar sojojin Nigeria a yankin ta kara da cewa sojojin sun kashe mahara biyu sauran kuma suka tsare a jirgin da suke tukawa. Har'ila yau an kara yawan sojoji a yankin tare da karin kayan aiki wadanda suka hada da jirgaen ruwa masu tsananin gudi, sannan sun ce zasu kama wadanda suka aikata wannan kisan don fuskantan sharia.