Gabon : Kotu Ta Hanawa Al'umma Zabinsu, Inji Jean Ping
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11542-gabon_kotu_ta_hanawa_al'umma_zabinsu_inji_jean_ping
Dan takara daya sha kaye a zaben shugaban kasa a Gabon, Jean Ping, ya yi wasti da hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke wanda ya tabbatar da Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 25, 2016 02:16 UTC
  • Gabon : Kotu Ta Hanawa Al'umma Zabinsu, Inji Jean Ping

Dan takara daya sha kaye a zaben shugaban kasa a Gabon, Jean Ping, ya yi wasti da hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke wanda ya tabbatar da Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

A wani taron manema labarai a jiya Asabar Mista Ping, ya ce kotun tsarin mulkin kasar ta hanawa al'ummar Gabon zabinsu, tare da danganta demukuraddiyar kasar da ta'adanci.

Mista Ping ya yi wannan firicin ne sa'o'i kadan bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sake zaben Ali Bongo Ondimba a mastayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 27 ga watan Agusta daya bar baya da kura.

A wata hira da yayi da kanfanin dilancin labaren Reuters, zababen shugaban kasar Ali Bongo ya ce zai kafa gwamnati wace zata kunshi dukkan bangarori ciki har da 'yan adawa, bugu da kari har da babban abokin hammayar na shi Jean Ping idan yana bukatar hakan.

A Jiya ne kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukunci akan jayayyar dake tsakanin bangarorin biyu kan zargin tafka magudi a zaben, wanda ya sa har kotun ta kai ga sake kirga kuri'un da aka a zaben.