Mayakar Kungiyar Al-Shabab Na Kasar Somaliya Sun Yi Rauni
Ministan harkokin wajen kasar Somaliya ya ce: Hadin kan sojojin gwamnatin Somaliya da dakarun hadin gwiwa da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar ya yi sanadiyyar raunana kungiyar Al-Shabab.
A jawabinsa a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya Abdus-Salam Umar ministan harkokin wajen kasar Somaliya ya bayyana cewa: Sojojin gwamnatin Somaliya da dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasar ta "AMISON" sun yi nasarar raunana kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab, inda a halin yanzu yankunan da suke karkashin ikon kungiyar bai kai kashi 10 cikin 100 ba, sannan mafi yawan kwamandojin kungiyar sun halaka a gafen yaki, yayin da wasu suka fice daga kungiyar.
Abdus-Salam ya kara da cewa: Hare-haren wuce gona da iri da mayakan kungiyar Al-Shabab suke kai wa wasu yankunan Somaliya ko kasashen makobta karfin hali ne kawai na neman a ce suna ci gaba da wanzuwa.